IQNA

Kyautar Kur’ani Ga Masu wasanni Sinima A Senegal

23:08 - June 23, 2018
Lambar Labari: 3482782
Bangaren kasa da kasa, an bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki ga wasu fitattun masu wasan sinima a kasar Senegal.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal Sayyid Hassan Ismati ya mika kyautar kwafin kur’ani mai tsarki ga wasu fitattun ‘yan wasan sinima na kasar.

An bayar da wannan kyauta ne da nufin karfafa gwiwar wadannan ‘yan wasa wadanda dukkanin mabiya addinin muslucni ne.

Akasarin fina-finan sinima da suke gabatarwa dai suna da alaka da lamurra da suka shafi addinin muslucni da tarihin muhimman mutane da suka taka rawa a cikin yaduwar addinin muslunci.

Aisha jah na daga cikin wadanda suka samu wannan kyauta, kuma shugaban karamin ofishin jakadancin Iran ya bayyana cewa, a shirye yake ya karfafa alaka ta fuskar fina-finai tsakanin kasashen biyu a bangaren fina-finan musulunci.

3724588

 

 

 

 

 

captcha