IQNA

Ansarullah Ta Ce Bata Da Matsala Matukar dai MDD Za Ta Kula Gabar Hudaidah

23:56 - June 22, 2018
Lambar Labari: 3482780
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Ansarullaha  Yemen ta ce ba ta da wata matsala domin mika tashar jiragen ruwa ta Hudaida ga majalisar dinkin duniya matukar dai za ta iya kula da ita.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da jagoran kungiyar Ansarullah ke jawabi, ya tabo batun yunkurin da majalisar dinkin duniya take domin ganin an kawo karshen artabun na Hudaidah kuwa, Alhuthi ya ce tun daga lokacin da makiya al'ummar kasar yemen suka fara kaddamar da hari kan kasar fiye da shekaru uku da suka gabata, ba su taba kin amincewa da tattaunawa ta siyasa ba.

Ya ce amma matsalar ita ce majalisar dinkin duniya ba za ta iya yin komai ba, domin kasashen da suke da tasiri a kanta ko dai suna goyon bayan masu kai hare-hare  saboda sayen makamai da suke yia  a wurinsu, ko kuma su kansu suna daga cikin masu yi wa makiya al'ummar Yemen wannan aiki na rusa kasar ta Yemen, domin su ci gaba da karbar biliyoyin kudaden man fetur daga hannun makiya al'ummar Yemen ta Yemen, y ace amma idan majalisar dinkin duniya tana ganin za ta iya kula da wurin za su iya mika mata shi.

Dangane da zargin da Amurka da wasu 'yan korenta da suek kaddamar da hari a kan kasar ta Yemen suke yi na cewa Iran tana aikewa da makamai zuwa yemen ta hanyar tashar jiragen ruwa Hudaida kuwa, Alhuthi ya ce wannan yana  a matsayin wawantar da al'ummomin duniya ne, domin kuwa dukkanin jiragen ruwa da suke isa Hudaidah, tun a cikin ruwa sai jiragen ruwan yaki na makiya al'ummar yemen sun tare su, tare da bincike dukkanin abin da suke dauke da shi kafin su su isa Hudaida.

3724440

 

 

 

captcha