IQNA

Matakan Buga Kur’ani A Kasar Masar

23:58 - June 21, 2018
Lambar Labari: 3482777
Bangaren kasa da kasa, madaba’antu da daman a kasar Masar suna buga kur’ani bisa ruwayoyin kira’a daban-daban.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, kamar yadda aka saba madaba’antu da daman a kasar Masar suna buga kur’ani bisa ruwayoyin kira’a daban-daban musamman ma dai kirara warsh.

Wannan kira’a dai ita ce tafi yaduwa  akasashen arewacin Afirka, da suka hada da kasar Masar, Morocco, Tunisi, Aljeria da kuma kasar Libya, da ma wasu daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka

A kan yi aiki buga kur’ani a kasar Masar isa matakai biyar, dukkanin matakan na tantancewa ne, domin tabbatar da cewa ba a buga kur’ani a kan kure ba.

3724335

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha