IQNA

Kwamitin Tsaron MDD Zai Gudana Da Zama Kan Batun Yemen

23:57 - June 18, 2018
Lambar Labari: 3482770
Bangaren kasa da kasa, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zai gudanar ad zama kan batun rikicin kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, martin Griffiths manzon musamman na majalisa dinin duniya kan rikicin Yeman, a yammacin yau zai halaci zaman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wanda zai gudanar kan batun rikicin kasar Yemen a asirce.

Zaman zai duba batun shawarar da majalisar dinkin duniya ta gabatar wa kungiyar Ansarullah ne kan ta janye daga gabar ruwan Hudaida da kasashen da suke yaki da yemen suke son karbewa, shawarar da Ansarullah suka ki amincewa da ita, amma dai sun bukaci a basu lokac su yi tunani kan wasu batutuwan da aka gabatar musu.

Martin Griffiths manzon musamman na majalisa dinin duniya kan rikicin Yeman a yau ne yake barin birnin San’a domin halartar zaman taron na kwamitin tsaro.

3723453

 

 

 

 

captcha