IQNA

Mai Yiwuwa A Canja Lokacin Kiran Sallar Isha’i A Saudiyya

23:49 - March 18, 2018
Lambar Labari: 3482486
Bangaren kasa da kasa, majalisar kasar Saudiyya za ta yi dubi kan wata shawara da wasu ‘yan majalisa suka bayar kan a rika jinkirta lokacin kiran sallar Isha’i.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Riyad ta bayar da rahoton cewa, bayan wata shawara da wasu ‘yan majalisa su 25 suka bayar kan a rika jinkirta lokacin kiran sallar Isha’i majalisar kasar Saudiyya za ta yi dubi kan wannan batu.

Shawar dai tana magana ne kan a rika jinkirat kiran sallar isha’i e har zuwa saoi biyu bayan kammala magariba, musamman a manyan birane, sakamakon yadda hakan yakan saka ‘yan kasuwa cikin gaggawa a lamrinsu saboda lokacin yana kure musu.

Wannan yazo bayan umarnin da yariman saudiyya saurayi mai jiran gado ya bayar e, kan cewa  adaina takura ma ‘yan kasuwa kan rufe shagunansu a lokacin salla.

3700663

 

 

 

captcha