IQNA

Taliban Ta Dauki Nauyin Harin Da Aka Kai A Kabul

22:52 - March 17, 2018
Lambar Labari: 3482483
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin bama-baman da aka kaddamar a birnin kabul fadar mulkin kasar Afghanistan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, kamfadilalncin labaran Shuruq ya bayar da rahoton cewa, zabihullah Mujahid kakakin kungiyar taliban ya bayyana cewa su ne suka kaddamar da harin bama-bamai a birnin Kabul.

Kafin wanann lokacin dai kakain ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar Afhhanistan Nusrat Rahimi ya sanar da kai harin, duk da cewa bai tabbatar da wanda suka kai harin ba, amma ya ce ana zargin kungiyar ta Taliban da hannu a harin.

An kai harin ne dai da wata mota da aka shakare da bama-bamai a jiya a cikin birnin kabul, wanda ya nufi wasu sojojin Birtaniya, amma a cewar mahukuntan Afghanistan harin bai same su ba, amma dai wasu fararen hula biyar sun rasa rayukansu, wasu kuma sun jikkata.

3700626

 

captcha