IQNA

Hardar Kur’ani Ta Hanyar Rubutun Allo A Libya

21:27 - March 16, 2018
Lambar Labari: 3482478
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen hardar kur’ani mai tsarki a kasar Libya ita ce hanyar rubuta kur’ani a kan allo.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na akhbaralaan.net cewa, cibiyar Abrar tana daya daga cikin fitattun cibiyoyi na hardar kur’ani mai tsarki a kasar Libya wadda take yin amfani da rubutu a kan alluna wajen koyar da harda.

Malamai masu koyarwa a wannan cbiya da sun yi imanin cewa, yin afani da wannan hanya yafi sauki wajen samun damar hardae kur’ani mai tsarkia  ckin sauri.

Ana yin amfani da alluna ne da aka sassaka daga itace masu kwari, inda akan rubuta ayoyin kur’ani mai tsarki bisa tsarin surori masu sauki daga kasa sai ayi sama, har sai an kai karshen kur’ani a hankali.

Muhammad Sashu daya ne daga cikin malamai masu koyarwa a wannan cibiya ya bayyana cewa; sun gaji wannan salon a karatun kur’ani da harda ta hanyar yin amfani da allo daga iyaye da kakanninsu ne, kuma wannan hanya tana da sauki sosai.

Baya ga kasar Libya, mafi yawan kasashen larabawan arewacin Afirka da kuma kasashen yammacin Afirka, duk suna yin amfani da wannan salon a karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki.

3700344

 

 

 

 

captcha