IQNA

Wanda Ya Jagoranci Juma’a A Tehran:

Maganganun Wawanci Na Trump Sun Sake Mayar Da Hankulan Mutane Ga Batun Quds

22:23 - December 15, 2017
Lambar Labari: 3482202
Bangaren kasa da kasa, Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran, Hujjatul Islam wal Muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana cewar makiya sun kirkiro kungiyar Da'esh (ISIS) ne da nufin tabbatar da tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila, to sai dai sun gagara cimma wannan bakar aniya ta su.

 

Hujjatul Islam wal Muslimin Kazim Siddiqi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a birnin Tehran a yau inda ya ce makiya al'ummar musulmi sun kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Daesh ne da nufin haifar da fitina a tsakanin musulmi don haramtacciyar kasar Isra'ila ta samu zaman cikin aminci da kwanciyar hankali, to sai dai sun gagara cimma wannan bakar aniyar  ta su, sannan kuma ta hakan Iran ta kara samun irin tasiri da fadi a ji da take da shi a yankin Gabas ta tsakiya.

Yayin da ya koma kan Palastinu da kuma birnin Qudus kuma, Na'aibin limanin Juma'ar ya bayyana cewar lamarin Palastinu shi ne babban kuma mafi muhimmancin lamurran duniyar musulmi, yana mai yin Allah wadai ga matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Sheikh Siddiqi ya kara da cewa babbar manufar makiya na haifar da rikici a duniyar musulmi ita ce shagaltar da musulmin da kansu don su manta da lamarin Palastinu wanda ya ce musulmi ba za su taba mancewa da wannan lamarin ba.

Wanan mataki na Donald Trump dai ya sanya hankulan alummomin duniya ya sun koma ga batun Palastinu da kuma irin zaluncin da al’ummar Palastinu take fuskanta na tsawon shkaru, tare da juya hankulan musulmi da kiristoci ga batun masallacin quds mai alfarma.

3672836

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha