IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Da Kisan Masallata A Afirka ta Tsakiya

23:40 - October 15, 2017
Lambar Labari: 3482002
Bangaren kasa da kasa, maalisar dinkin duniya ta yi llah wadai da kisan da aka yi musulmi 25 da suke yin salla a cikin masalalci a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anatoli cewa, tawagar majlaisar dinkin duniya a kasar Afirka ta tsakiya ta yi kakkausar suka dangane da kisan da aka yi wa wasu musulmi a lokacin da suke yin sallah a cikin masallaci.

Bayanin tawagar ya ce hakika abin da ya faru ba abu ne da za a lamunce da shi ba, saboda haka za adauki kwararan matakai domin ganin ganin irin haka bata sake faruwa ba.

Wannan tawagar ta bayyana cewa wasu masu dauke makamai mabiya addinin krista ‘yan kungiyar anti balaka, sun kaddamar da harin a wani kaue, inda suka samu mutane suna yin salla a cikin masalaci, a nan take sukakashe limamanin da na’ibinsa da kuma wasu masallata fiye da ashirin.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta anti balaka tana fakewa da sunan addinin kirista wajen aikata ta’addanci a kan musulmi, duk kuwa da cewa akwai kirsitoci da dama akasar da basu yarda da abin da kungiyar take yin a ta’addanci da sunan addinin kirista ba.

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na daga cikin ksashen nahiyar Afirka masu arzikin ma’adanai, amma yakin da ake fama da shi ya daidaita kasar.

3652880

captcha